Abin da zai faru a babban taron APC na gobe Asabar...
Apc.
Abin da zai faru a babban taron APC na gobe Asabar...A Najeriya, a gobe Asabar ne jam`iyyar APC mai mulki ke babban taronta na kasa, inda wakilai daga sassan kasar za su zabi sabbin shugabannin da za su gudanar da harkokin jam`iyyar nan da shekaru hudu masu zuwa.
Mutum tara ne suka nuna sha`awar takarar shugabancin jam`iyyar, amma jiga-jiganta sun yanke shawarar bin hanyar maslaha yayin zaben.
Sau biyu ana saka rana ana dage ranar taron bayan an ci wani zamani ana hayaniya da ta da kura.
Bakwai daga cikin mutum tara da ke takarar sun fito ne daga arewa ta tsakiyar Najeriya. Su ne: Mallam Saliu Mustapha, Mallam Mohammed Etsu, Senata Mohammed Sani Musa, Senata Tanko Al-Makura, Senata George Akume, Senata Abdullahi Adamu.
Sai na takwas, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari daga shiyyar arewa maso yamma. Sannan akwai Senata Ali Madu Sharif, wanda `yan kwanaki gabannin taron ya ce ya janye.
Sai dai mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, kuma jami`i a kwamitin yada labarai na babban taron ya ce maslaha za a bai wa fifiko.
Comments
Post a Comment
Barka da zuwa