: Abubuwa shida da suka kamata ku sani game da sabon shugaban APC
Wakilan jam'iyyar APC daga sassa daban-daban na Najeriya sun amince da tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar da ke mai mulkin kasar.
Abubuwa shida da suka kamata ku sani game da sabon shugaban APC
Gwamnan Jigawa Muhammadu Badaru ne ya sanar da hakan a yayin babban taron jam'iyyar bayan duka waɗanda suke takara sun janye wa Abdullahi Adamu.
Sanata Abdullahi Adamu, wanda da farko ba ya cikin waɗanda suka nuna sha'awar takarar shugabancin APC, daga bisani ya kutso kuma ya samu goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni.
Wannan goyon bayan ne ya tilasta wa sauran ƴan takarar shugabancin APC janye wa a ranar Asabar kafin shiga dandalin taron.
Ƴan takarar da suka janye sun da tsohon gwamnan Benue George Akume da tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura da tsohon gwamnan Zamfara Abdul'Aziz Yari Abubakar da Saliu Mustapha d kuma Etsu Muhammed.Sanata Abdullahi Adamu ya zama sabon shugaban Jam'iyyar APC
Abubuwa shida da suka kamata ku sani gabanin babban taron APC
Sanata Adamu ya zama sabon shugaban APC ne fiye da shekara guda bayan sauke tsohon gwamnan jihar Edo Adams Oshiomhole daga mukamin da kuma nada Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin riko na jam'iyyar.
Wane ne Abdullahi A
damu?Sanata Adamu tare da tsoffin shugabannin APC biyu ( Edo Adams Oshiomhole da John Oyegun
Abdullahi Adamu yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya kuma sau biyu yana zama gwamna a jihar ta Nasarawa.
Ya rike mukamin gwamnan jihar Nasarawa ne daga sekarar 1999 zuwa 2007. Hasalima shi ne gwamnan farar-hula na farko a jihar.
An haife shi a garin Keffi da ke jihar Nasarawa kuma ya yi karatunsa na firamare da Sakandare a jihar Nasarawa da kuma Benue ta yanzu a daga 1960 zuwa 1962.
Ya kuma yi karatun gaba da Sakandare a Kwalejin Fasaha, Bukuru, da kuma Kwalejin Fasaha da ke Kaduna wato Kaduna Polytechnic inda ya samu Babbar Difiloma.
A shekarar 1992, ya kammala Digirinsa na farko a fannin Lauya a Jami'ar Jos kuma ya zama lauya a 1993.
Sanata Adamu ya soma siyasa a 1977, kuma ya rike mukamai da dama.
Ga abubuwa shida da suka kamata ku sani game da sabon shugaban jam'iyyar APC:
Comments
Post a Comment
Barka da zuwa