Da Dumi-Diminsa :- Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Abubakar Yari, ya Rabawa Talakawan Jihar Tallafin Abinci, Domin shiga Ramadan.
Da Dumi-Diminsa :- Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Abubakar Yari, ya Rabawa Talakawan Jihar Tallafin Abinci, Domin shiga Ramadan.
A yau Alhamis mai girma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdul'aziz Yari Abubakar, ya raba kayan masarufi zuwa ga illahirin al'ummomin jihar Zamfara dake Kananan Hukumomi goma sha hudu (14LGA) dake jihar Zamfara kamar yadda ya saba a kowace shekara domin samun sauki, walwala da jin daɗin gudanar da Azumin watan Ramadan.
Mai girma tsohon Sanata mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya a zauren Majalisar Dattawan Nijeriya a Majalisa ta takwas (8 Assembly) Distinguished Senator Kabiru Garba Marafa, CON (Marafan Gusau) tare da rakiyar Hon.Lawal M. Liman (Gabdon Kaura), His Excellency, Hon.Mukhtar Shehu Idris (Kogunan Gusau) shi ne ya kaddamar da tallafin Buhuhuwan Abinci dubu hamsin da takwas 58,200 ga al’ummar jihar Zamfara a madadin mai girma Tsohon Gwamna Hon.(Dr.) Abdul’aziz Yari Abubakar (Shattiman Zamfara) a filin taro dake dabra da gidajen Gidan dawa a garin Gusau Babban birnin jihar Zamfara.
Ga Jadawalin Yadda Tallafin Ya Kasance;
1:- Shinkafa tirela 50
2:- Masara tirela 50
3:- Gero tirela 50
4:- Sugar tirela 22
Kowace Ƙaramar Hukuma an bata Buhun Shinkafa, Buhun Masara, Buhun Gero, Buhun Suga har Tirela 7.8, yayin da Karamar Hukumar Mulki ta Gusau mai yawan al’umma za ta anfana da Tallafin kaso biyun kowace ƙaramar Hukuma, wato (Tirela 15.6).
Haka zalika Mai girma tsohon Gwamnan jihar Zamfara Hon (Dr.) Abdul’aziz Yari Abubakar ya baiwa Kungiyar Zamfara Cycle Tirela 47 domin rabawa zuwa ga Ƴan Gudun Hijira a fadin jihar Zamfara.
Su ma Marayun jihar Zamfara sun anfana da wannan Tallafi, inda Mai girma tsohon Gwamna Hon. (Dr.) Abdul’aziz Yari Abubakar ya bayar da Tirela goma sha daya (11) zuwa ga Marayu Dubu takwas 8,000 da ke cikin Masarautu goma sha bakwai (17 Emirates) da ke fadin jihar Zamfara.
Muna rokon Allah (SWT) ya saka ma Mai girma (Shattiman Zamfara) da mafificin alkhairinsa, Allah (SWT) ya kara masa lafiya, arziki da daukaka, Allah (SWT) ya biya dikkanin bukatunsa na alkhairi saboda Annabi Muhammad (SAW).
Al’mansoor Gusau
Babban daraktan yada labarai na Tsohon Gwamnan JZamfara Alh Abdul'aziz Abubakar Yari.
Daga Al'mansoor Gusau.
Kuci gaba da Bibiyar wannan website din namu domin kawo muku Nishadi,Labarai,Rahotanni da sauransu, sannan kuyi Following namu kuyi mana comment, domin Jin dadin labarin ko Akasin haka, domin samun Sababbi Idan mundora.
Comments
Post a Comment
Barka da zuwa