DA_DUMI_DUMINSU Rundunar sojojin Najeriya ta ce ba za ta lamunci labaran boge da ake yaɗawa da sunan jami'anta ba a shafukan sada zumunta.
'Za mu kare 'yancin dimokuraɗiya'
Brigediya Tukur ya ce a ranar Asabar suka soma ganin rubutun a shafukan sada zumunta, kuma suna zargi wani da ke ganin ba a yi masa daidai ba ne ya ke daukan nauyin yaɗa labaran.
Ya ce a wannan hali da ake ciki bai kamata a ɓata sunan rundunar tsaro ta Najeriya ba.
Shiyasa suka fito suka nemi waɗanda ke yaɗa wannan batu na soja na tattauna da 'yan siyasa, su fito su yi bayyani inda suka samu labarinsu.
"Muna kalubalantar masu yadawa zance su fito su fadi inda suka samu bayanansu.
"Sannan za a gayyaci mutane domin amsa tambayoyi. Saboda a wannan hali bai kamata a bata sunan rundunar sojin kasa ba.
"Mun yi ammana da tsarin mulkin dimokuraɗiya da dokokinta. Kuma zamu yaki duka bin da zai kawo wat sarin mulkin karan-tsaye."
Brigediya Tukur ya ce, akwai tsiraru da ke kokarin amfani da rundunar sojan Najeriya domin kawo rudani, amma dai su na sanar da su cewa ba za su yi nasara ba.
Rundunar ta ce duk wani abu da zai kasance matsala ga mulkin dimokuradiya za su dakile shi.
Sannan ya ce hakkinsu ne kare dimokuraɗiya da ‘yancita, shiyasa ba zau lamunci duk mai kokarin haifar da tunzuri ba.
Ya ce shi ba zai faɗi sunan kowa a bakinsa ba, amma dai ana bincike domin hukunta duk masu laifi.
Comments
Post a Comment
Barka da zuwa